(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Zaben2019: Duk bakin cikin su sai na siyar da NNPC – Atiku Abubakar

Karatun minti 1

Dan takarar shugabancin kasa karkashin inuwar jami’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya kara jaddada matsayinshi na cefanar da hukumar NNPC, abinda ya kira babu gudu, ba ja da baya.

Atiku yace talakan Najeriya baya amfana daga kamfanin na NNPC, kuma nan ne matattarar cin hanci da rashawa.

Tsohon mataimakin ya kara da misali akan siyar da kamfanin NITEL, shine yayi silar yan Najeriya suke mallaki wayar salula tare da shigowar kamfanunuwan sadarwa cikin kasa tare da bada guraben aikin yi ga al’ummar kasa.

Jaridar Daily Trust ta rawaito tsohon mataimakin shugaban kasan ya alkawaranta bada tallafin karatu ga wadanda suka chanchanta tare da bawa matasa mukamai kaso 30 cikin dari a gwamnatinshi.

Ko yaya al’ummar Najeriya suke kallon wannan batun?

Zaku iya bayyana ra’ayoyinku a shafinmu na Facebook.

 

 

Karin Labarai

Sabbi daga Blog