Zuwan Buhari Kano: Shin Buhari yana goyon bayan ‘yan rashawa?

A cigaba da yakin neman zaben shugaba Muhammadu Buhari, yau na sauka a garin Kano domin tallatar manufarshi ta sake tsayawa shugabancin kasar a zabe mai kamawa.

Al’ummar jihar ta Kano dama Najeriya baki daya, sunyi zaman dakon irin hukunci da zai dauka. Tambayar itace: Shugaba Buhari zai goyi bayan sake zaben gwana Abdullahi Ganduje? ko zai barranta dashi yacewa mutane su zabi chanchanta?.

Taron daya gudana a filin wasa na Sani Abacha dake tsakiyar birnin Kano, shugaba Buhari yace to “Kanawa ga Gandujenku nan”, hakan na nufin shugaba Buhari baya goyon bayan gwamna Ganduje?

Alkaluma sun nuna shugaban baya tare da Gwamnan Kanon, a baya-bayan nan shugaba ya hada tarurruka da hada da ganawa da duk ‘yan takarkarun gwamna karkashin inuwar ta jami’iyyar APC.

Masu Alaƙa  Zuwan Buhari Kano: Barranta rashawa ko goyon bayanta?

Kwatsam daga kusan karshen taro, sai ga shugaba Buhari ya daga hannun gwamnan da ake zargi da karbar na goro.

Shugaba Buhari lokacin daga hannun Ganduje

Shin menene daga hannun dan takara a siyasance?

Shugaba Muhammadu Buhari mutum ne da Allah yayi farin jini musamman a arewacin Najeriya, domin kuwa a shekarun bayan duk wanda Buharin ya daga hannunshi yana samun nasara saboda amincewar da talakawa sukayi masa.

Babban Misalin haka:

Shekarau a shekarar (2003-2011)          ANPP

Isa Yuguda (2007-2015)             

Bukar Abba Ibrahim (1999-2007)

Mammam Bello Ibrahim (2007-2009)

Daga hannun a siyasance yana nufin goyon bayan dan takara dari bisa dari, hakan ce take sa duk wanda yaje taro da Shugaba Buhari, burinshi kar a tashi daga taron bai daga hannunshi ba.

Masu Alaƙa  Akwai yiwuwar sake komawa wa'adina na biyu da wasu tsofaffin Ministocina - Buhari

Daga hannun Ganduje yana nufin Shugaba Buhari yana goyon bayan ‘yan rashawa?

Ta rage gare ka domin yi bincike.

Munsan dai Buhari mai gaskiya ne!

Sako na musamman

Shin kuna da wata sanarwa ko bukatar bamu labari?

Ku aiko mana da sako ta submit@dabofm.com

%d bloggers like this: