Abdulbasit Umar dan shekara 22 tare da abokansa su 2, sune Hukumar ‘Yan Sandan jihar Taraba ke tuhuma da sace ‘kanwarsa yar kimanin shekaru 10 Amina Umar a hanyar ta ta zuwa makaranta.
Abdulbasit, tare da Sadiq Sani da Abdullahi Habib, sun bukaci kudi har naira miliyan 10 a hannun mahaifinsa matsayin fansa kafin su sake ta.
Kakakin hukumar yan sandan jihar, DSP David Misal, wanda ya bayyanasu ga manema labarai tare da wasu mutane 12 da ake zargi da garkuwa da mutane da kuma fashi da makami ya yi bayanin cewa jami’an tsaro sun damkesu ne yayinda suka tafi amsan kudi N4million da aka yarje daga baya.
Jaridar Daily Nigerian ta bayyana cewa da yake bayyana dalilinsa ga manema labarai, Abdulbasit ya bayyana cewa “Ban taba aikata irin wannan abu ba amma na bukaci kudin ne domin fita kasar waje karatu.”
“Manufata itace idan na amsa kudin, zan tafi karatu kasar waje.”
Daya daga cikin abokansa da suka aikata laifin, Sadiq Sani, ya ce kawai shi ya taya abokansa ne domin karban kudi daga hannun mahaifinsa.
