Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya dora alhakin kashe-kashen dake faruwa wanda yan kungiyar Boko Haram da sauran yan ta’adda keyi a kwana-kwanan nan a arewacin Najeriya musamman a jihohin Katsina, Borno kan kullen annobar Koronabairos.
Wannan na zuwa dai dai lokacin da shugaba Buhari ke bada sakon bikin zagayowar ranar dumokuradiyya, DABO FM ta jiyo shugaban na fadin hare haren yan ta’addan ya samu wajen zama ne daga kullen annobar Kwabid19, inda ya kuma nuna takaicin sa akan hare haren.
Buhari ya ce “Duk kananun hukumomin dake hannun Boko Haram na jihohin Borno, Adamawa da Yobe tini muka yi nasarar kwato su, wanda a baya ‘yan wadannan garuruwa aka kore su zuwa nesa.”
“Ina mai nuna rashin jin dadi da kashe-kashen da ya auku a kwana kwanannan a Katsina da Borno, wannan ya faru ne sanadiyyar takaita zirga zirga da muka yi saboda annobar Kwabid19. Nan bada jimawa ba jami’an tsaro za su kamo gami da gurfanar da masu hannu a ciki.” – Shugaba Muhammadu Buhari a jawabinshi na ranar Juma’a.
Daga karshe shugaban ya aike da sakon ta’aziyya ga ‘yan uwan wadanda suka rasa rai dama wadanda suka jikkata.
