0
Hukumar zabe ta INEC ta dage gudanar da zaben ‘yan majalissun jiha a wani shashi na jihar Adamawa bisa rasuwar Adamu Kwanate.
Kwanate dan jami’iiyar APC ya rasu ne yayin da ana tsaka da yakin neman zabe ranar Laraba a jihar Adamawa. Ya kasance shine dan majalissar jiha mai wakiltar Nasarawo/Binyeri (Mayo Belwa 1).
Sanarwar dage zabe ta fito ne a daren jiya juma’a, lokacin daya rage sauran awanni kafin a fara gudanar da zaben a safiyar Asabar.
