(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Zaben Gwamna: Jami’an tsaro sun damke wata mota dankare da kudade a Sokoto

Karatun minti 1

A cigaba da gudanar da zaben gwamnoni hadi dana ‘yan majalissun jiha, jami’an tsaro sun damke wata babbar mota wacce take cike da kudi.

Jami’an tsaro hadi dana hukumar EFFC sun kama motar, kirar Jeep, mai lamba ABC 924 LU, yayinda take tafiya a kan titin  Garba Duba a tsakar daren jiya Juma’a.

Tini dai jami’an suka bada umarnin girke motar a hedikwatar ‘yan sanda dake jihar ta Sokoto domin yin kyakkyawan bincike.

Motar dai na dauke da buhuhunan kudade masu tarin yawa.

Manema labarai sunyi kokarin jin ta bakin hukumar ‘yan sandan amma hakan yaci tura, kamar yadda Gidan Rediyon BBC HAUSA ya bayyana a shafinsu na yanar gizo-gizo.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog