0
Hukumar zabe ta INEC ta cire jadawalin adadin akwatinan da aka soke zaben su saboda dalilan hargitsi da kuma yin zabe adadin daya dara na mutanen dake da rijista a wannan akwati.
Za’a sake zaben ne a akwatina 234 daga cikin kananan hukumomi 30 da hukumar ta soke zaben.
Kamar yadda zaku gani a takardar da hukumar INEC ta fitar a yau Talata a babban ofishinta dake birnin Kano.

