Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasiru El-Rufa’i ya bawa dukkanin mukarraban gwamnatinshi umarnin rubuta takardar ajiye aiki.
Jaridar The Nation ta rawaito cewa Gwamna ya bada umarnin ne ga dukkan ma’aikata ‘yan siyasa da suke cikin gwamnatin a cigaba da shirin kafa sabuwar gwamnati a jihar ta Kaduna.
[the_ad_placement id=”content”]
Gwamnan yace dole kowa ya tabbata ya rubuta takardar ajiye aiki kafin ranar 30 ga watan Afirilun 2019.
Majiyoyi sunce sauke jami’an gwamnatin da El-Rufa’i yayi zai taimakawa jihar wajen baiwa ma’aikatar kudi sauke duk nauyin da yake kanta kafin a shiga sabuwar gwamnati.
Haka kuma daga gefe guda gwamnan na nuni da cewa ba kowane jami’i ne zai samu komawa kujerarshi ba.
Saidai sanarwa ta ware wasu kwamishinonin ma’aikata na 8 wadanda babu su a ajiye aikin, sun hada da:
- Ma’aikatar Shari’a
- Hukumar Zaben jihar ta SIECOM
- Ma’aikatar Ruwa
- Hukumar Ma’aikata ta Civil Service
- Hukumar Tattara kudaden shiga ta FISCAL
- Assembly Commission
- Peace Commision
- Public Procurement Authority.
Sanarwa dai ta kara ware duk wanda baifi watanni 6 yana aiki ba, wanda suka hada da
- Babban Mai kula da Asusun jihar
- Pricipal Private Sectary
Da sauransu
