Majalisar tarayyar Turai ‘European Union’ ta bayyana cewa babu wani ci gaba a yakin da ake da yan ta’addan Boko Haram a fadin Najeriya.
Majiyar Dabo FM ta bayyana majalisar tarayyar Turai ta fadi hakan ne a ranar 16 ga Junairu biyo bayan yawan hare haren kan fararen hula da sojojin Najeriya, kamar yadda jaridar TheCable ta fitar.
Rahoton TheCable ya kara da cewa yan satittikan da suka gabata ne kungiyar ta’addan Boko Haram suka kai harin da ya hallaka mutane 11 domin ramuwar kisan da aka yiwa shugabannin kungiyar IS’, Abu Bakr al-Baghdadi, da Abul-Hasan Al-Muhajir.
Mutane da yawa suna tsaye suna kallo lokacin da jerin motocin kwamandan yan ta’addan yaje ya kai hari kan titin Damaturu zuwa Maiduguri inda suka kai hari cikin kauyukan dake gefen titinan.
Majalisar tace yanayin da Najeriya ke cike ya kara tabar-barewa fiye da da. Daga karshe dai Majalisar tarayyar Turai tayi kira da babbar murya ga mahukuntan Najeriya da su kula da hakkin dan adam, yara dana addinai.
