Siyasa

Kwankwaso bashida takardun kammala Firamare – Ganduje

Dr Abdullahi Ganduje

Mai girma gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya kalubalanci tsohon gwamna Sen Rabi’u Kwankwaso daya fito da takardar kammala makarantar firamaren da yayi.

Gwamna Ganduje ya karada cewa tsohon gwamnan bai zama injiya cikakke ba domin shima bashida shaidar kammala karatun.

“A wace makaranta ya kammala karatun injiniyancin?”

“Ina mamakin mutumin da bai ci jarabawar Common Entrance ba kuma zai kalubalanci yadda gwamnatinmu take tafiyar da harkar ilimi a jihar Kano, bayan muna tare da Profesosi da masu shaidar digirin digir-gir.”

Tin a bayan barkewar Kwankwaso da Ganduhe suka ta jefawa juna magana.

Kwanaki kasa da uku ya rage domin gudanar da zaben gwamna jihohin Najeriya.