//
Wednesday, April 1

Duk shifcin-gizo gwamnoni keyi a batun biyan Sabon Albashi -Kungiyar Kwadago

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Kungiyar kwadago ta bayyana cewa tun bayan zartar da mafi karancin albashi na N30,000 wata 8 da suka wuce, jihohi 5 ne kawai ke biyan sabon albashin.

Rahoton Dabo FM ya bayyana cewa kungiyar kwadago ta sanar da hakan ne bayan fitowa daga wani taro daya gudana a babban birnin tarayya dake Abuja.

Jihohin 5 sun hada da Jigawa, Kaduna, Adamawa, Kebbi da Lagos. Kamar yadda sanarwar wadda shugaban kungiyar ta kasa, Ayuba Wadda ya rattabawa hannu tare da sauran shugabannin ta.

Jihohin da suka nuna ko in kula, Bauchi, Yobe, Rivers, Benue, Gombe, Kwara, Imo, Osun, Ekiti, Oyo, Anambra, Taraba, Cross River, Ogun, Enugu, Nasarawa, Plateau, Kogi da Delta.

Masu Alaƙa  An fara zanga-zangar kifar da gwamnatin Buhari, Jami'an tsaro su kawo dauki -Uzodinma

Shugaban kungiyar ya kuma ja kunnen jihohin da cewa sun basu 31 ga Disamba itace ranar karshe idan har basuyi wani abu akai ba kungiyar zata dauki mataki.

Karin Labarai

Share.

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020