Siyasa

KANO: Zamu kama duk wani dan siyasa, mai kalaman tada hargitsi – Hukumar ‘yan sanda

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano karkashin jagorancin kwamishina Muhammad Wakili, ta fitar da gargadi akan yan siyasar da suke kalamai da ka iya tada fitina.

Gargadin da hukumar ta fitar ta hannun mai magana da yawun rundunar DSP Haruna Abdullahi.

Takardar mai lamba CZ: 5700/KS/PRD/VOL.3/48

“Muna gargadin duk wani dan siyasa da ke kalaman tada fitina, raba makamai ko rabawa matasa kwayoyi domin amfani dasu wajen aikata laifuka a lokacin gudanar da gangamin yakin neman zabe.”

Hukumar kuma tace bazata sassautawa duk wani dan siyasa ba duk matsayinshi a gwamnati ko masoyanshi a gari. Dole ne ‘yayan kowacce jami’iyya su bi ka’i’dojin da aka shimfida lokacin da aka kulla yarjejeniyar tabbatar da zaman lafiya.

Tace tini ta fara bincike akan maganganun da wasu yan siyasa sukayi, kuma da zarar ta gama zata aikesu zuwa gaban kuliya manta sabo domin fuskantar hukunci kamar yadda doka ta tanada.

Takardar da hukumar ta fitar.
Takardar da hukumar ta fitar.

Karin Labarai

Masu Alaka

Dokar hana cakudar Maza da Mata a baburan ‘Adaidaita Sahu’ tana nan daram – Ibn Sina

Dabo Online

Kano: CP Wakili ya kama ‘Yan fashi da masu dillancin Kwayoyi 142 a kwana 4

Dabo Online

Jirgin Kasa ya bi takan wasu mutane a jihar Kano

Kano: Ni yakamata a zaba – Muhammad Abacha

Dangalan Muhammad Aliyu

Akwai yiwuwar dasa abubuwan fashewa a guraren zabe, kasuwanni da guraren bauta – Masu Sa’idon Zabe

Dabo Online

Kiru/Bebeji: Baza mu mara wa Kofa baya ba a zaben ranar Asabar -Dattijan APC

Muhammad Isma’il Makama
UA-131299779-2