Taskar Matasa: Ga wanda suke tunani mai kyau, Daga Umar Aliyu Fagge

dakikun karantawa

A sati biyun da suka shude ne alummar Najeriya suka fito domin kada kuri’ar su ga mutumin da suka ga ya dace ya mulke su a matakin shugaban kasa, sanatoci, da yan majalisun tarraya.

Alhamdulillah anyi zabe cikin lumana duba da cewa nagartar dan takarar jam’iyya mai mulki yafi na sauran jami’iyyu.

Idan muka sauko kasa a matakin jihar Kano zamu ga cewa alumma basu fito yin zabe yadda ya kamata ba, duba da cewa babu hammaya dangane da zaben shugaban kasa.

A adadin kuri’u miliyan biyar (5m) da mutanen jihar Kano suka yi, kimanin kuri’u miliyan daya da dari bakwai (1.7m) ne kawai akayi amfani dasu a jihar Kano, shin ina sauran kuri’un suke?

Kuma sanin kowa ne cewa dukkan alummar da suke son shugaba Buhari da sauran yan gangan sun fito zabe a lokacin, yanzu kuma zabe ne tsakanin yan Gandujiyya da alummar gari.

Domin mutanen da suka zabi shugaba Buhari a sati biyun da suka gabata zai yi wuya su zabi Ganduje saboda manufar su ba daya ba ce : “Yaki da rashawa, shi kuma wannan karbar rashawa.”

A wannan satin mai zuwa ne alummar jihar Kano zasu yi fitar dango, gurin tabbatar da zabar nagartaccen dan takarar gwamna ba wanda ake zargi da sunkume-sunkumen kudin waje ba. Domin sauran kuri’un da sukayi batan dabo zasu bayyana ga nagartaccen dan takara.

Allah ya bamu ikon zabar cikakke, nagartaccen dan takara ba wanda zai taimaka gurin gurbacewar tarbiyar yara ba, domin gaskiya akwai bukatar alumma suyi tsayuwar daka gurin ceto jihar kano daga halin da take ciki a wannan shekarun.

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog