Siyasa

Har yanzu Abba Kabir Yusuf muka sani a matsayin dan takarar gwamnan PDP – INEC

A yammacin yau na ranar alhamis, wata babbar katu dake zaune a jihar Kaduna, ta tabbatar da ingancin zaben cikin gida da jami’iyyar PDP ta gudanar na fidda dan takarar gwamnan jihar Kano.

Kotun ta kara tabbatar da Abba Kabir Yusuf a matsayin halattacen dan takarar gwamnan jihar Kano a karkashin inuwar jami’iyyar PDP.

Daga shafin hukumar INEC, sunan Abba K Yusuf a cikin jerin jadawalin 'yan takar-karun jihar Kano tare da jami'yyunsu.
Daga shafin hukumar INEC, sunan Abba K Yusuf a cikin jerin jadawalin ‘yan takar-karun jihar Kano tare da jami’yyunsu.

Daga bangaren INEC – Kwana 3 da suka gabata.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC tace har ila yanzu Abba Kabir Yusuf ne dan takarar gwamnan jihar Kano karkashin  jami’iyyar PDP.

Kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta wallafa, tace wakilinta yayi waya da mai magana da yawun hukumar, Festus Okeye akan labaran da sukayi ta yawo akan umarnin da kotu ta bayar na cire sunan Abba Yusuf a matsayin dan takarar jami’iyyar ta PDP.

“Har yanzu babu wani umarnin kotu daya zo mana akan cire sunan dan takarar (Abba Kabir Yusuf).”

“Idan ma umarnin kotun ya iske mu, munada lauyoyin da zasuyi nazari akan batun kafin mu aiwatar.”

Yau ne labarai sukayi ta yawo a kafafen sadarwa tare da wasu manyan jaridu da suka rawaito cire sunan Abba Kabir a matsayin dan takarar gwamnan jihar Kano a inuwar jami’iyyar PDP tare da rushe zaben fidda gwani da jami’iyyar ta gudanar a shekarar data wuce.”

Jaridun sun rawaito umarnin kotu na cewa jami’iyyar ta sake zaben fidda gwani cikin kwanaki kafin zaben gwamna da hukumar INEC take shiryawa.

Karin Labarai

Masu Alaka

Ganduje, Sarki Sunusi sun jagorancin daurin auren Zaurawa 70

Dabo Online

#JusticeForKanoKids: ‘Yan sanda sun sake kubutar da Yaran Kano 2 daga Anambra

Muhammad Isma’il Makama

Zamfara: Kotun ‘Allah Ya Isa’ ta kwace zabe daga APC da bawa PDP

Dabo Online

PDP ta zargi Buhari, INEC da shirin yin magudi

Dabo Online

Bata-garin mabiya Kwankwasiyya sun yi wa Sheikh Pantami ihun ‘Bamayi’

Dabo Online

#NigeriaDecides2019: Atiku yasha kashi a akwatin kofar gidanshi

Dabo Online
UA-131299779-2