Zaben Gwamna: An kama wata mota cike da dan gwalallun kuri’u a jihar Kano

Karatun minti 1

A cigaba da gudanar da zaben gwamnoni tare da ‘yan majalissun jiha a yau Asabar, jami’an tsaro sunyi arangama da wata mota cike da dangwallalliyar kuri’a a mazabar Magwan dake karamar hukumar Nassarawa.

Wani mai shedar gani da ido ya bayyana mana cewa mutane da aka gani a cikin mota, wasu ne da suke aiki tare da gwamnatin jihar Kano.

“Da zuwan motar mutane sukace basu yadda da ita ba, muka tambaya sai akace mana malaman zabe ne, da muka tsananta bincike mukace lallai sai an bude mana mungani kwatsam sai jami’an tsaro na ‘yan sanda suka hanamu.”

“Munyi kokarin budewa, munga kuri’u ne aka dangwalawa jami’iyyar APC.”

 

 

Karin Labarai

Sabbi daga Blog