Zaben2019: INEC ta dage zabe a jihar Adamawa bisa mutuwar ‘dan takara

Karatun minti 1

Hukumar zabe ta INEC ta dage gudanar da zaben ‘yan majalissun jiha a wani shashi na jihar Adamawa bisa rasuwar Adamu Kwanate.

Kwanate dan jami’iiyar APC ya rasu ne yayin da ana tsaka da yakin neman zabe ranar Laraba a jihar Adamawa. Ya kasance shine dan majalissar jiha mai wakiltar  Nasarawo/Binyeri (Mayo Belwa 1).

Sanarwar dage zabe ta fito ne a daren jiya juma’a, lokacin daya rage sauran awanni kafin a fara gudanar da zaben a safiyar Asabar.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog