(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Zaben2019: ”Yan daban’ APC sun afka wa tawagar Kwankwaso a Bebeji

Karatun minti 1

A cigaba da zagayen yakin neman zaben dan takarar gwamnan jihar Kano karkashin inuwar jami’iiyar PDP, Engr Abba Kabir Yusuf, yau Alhamis tawagar da tsohon gwamnan jihar Engr Rabi’u Kwankwaso yake jagoranta sukaje karamar hukumar Bebeji domin taron karshe.

Saidai a kan hanyarsu ta shiga garin Bebeji, wasu ‘yan bangar siyasa suka afkawa tawagar Kwankwaso da sare-sare da makamai masu muni.

‘Yan daban da ake zarginsu da kasancewa yaran ‘dan majalissar wakilai mai wakiltar karamar hukumar Kiru/Bebeji, Hon Abdulmuminu Jibrin Kofa Maliya.

Wani mai shedar gani da ido ya bayyana mana cewa, tawagar PDP na tafiya akan titin Kofa, bata garin suka tare hanya suna zage-zage tare da fara ji musu rauni.

Rundunar yan sandar jihar karkashin mai magana da yawun rundunar, DSP Haruna Abdallahi ta tabbatar da faruwar al’amarin, tace kuma tini ta aike jami’anta domin kwantar da tarzoma.

Ku biyo mu domin kawo muku maganar wadanda abin ya ritsa tare kuma da wadanda ake zargi da aikata al’amarin.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog