Hoton da kuke gani a sama, hoto ne da ya gama gari, ya kuma kayatar da mutane musamman masoya Sarkin Kano murabus, Muhammadu Sunusi II.
Sai dai mutane sun manta da gane matashin da ya zauna ya zana hoton da yakamata masoya Sarki mai murabus sunyi masa kyauta bisa namijin kokarin da matashin yayi.
Hoton ya ja hankalin mutane da dama musamman a lokacin da rikicin Sarkin mai murabus da gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya kara tsamarin da ya kai ga tsige Sarki Muhammadu Sunusi II.
Babban abin mamakin da ban sha’awa, shi dai wannan matashin bai wuce shekaru 19 zuwa 21 da daya ba.
A cikin shirin Taskar Matasa na DABO FM, mun zakulo matashi domin yaba masa bisa irin namiji kokarin da yake yi wajen yin zane mai kayatarwa da ban sha’awa.
Sunanshi Abbas Haruna Nabayi, dan asalin jihar Jigawa, mazaunin jihar Kano.
A tattaunawar da DABO FM tayi da matashin ya bayyana mana dan takaitaccen tarihinshi.
“Shekaru na 21, dan asalin jihar Jigawa, mazaunin jihar Kano.”
Matashin yayi zane-zane daban daban da suka yi fice. Ciki har da wanda yayi wa Alhaji Aliko Dangote, Naziru Ahmad, Ali Nuhu, Ahmad Musa da sauran fitattun mutane da ya hada da Larabawa da Turawan Yamma.
Ga wani rahoto da muka hada tin shekarar da ta wuce a kan matashin inda zaku ga zane-zane iri-iri da matashin ya dadi yana yi.

