Abba Kabir Yusuf ne sahihin dan takarar jami’iyyar PDP – PDP Kano

Karatun minti 1

Bayan raɗe-raɗin da yayi yawo a kafafen sadarwa dama wasu manyan jaridun Najeriya na cire sunan dan takarar gwamnan jihar Kano karkashin inuwar jami’iyyar PDP, Engr Abba Kabir Yusuf.

Saidai shugaban riko na jami’iyyar PDP na jihar Kano, Engr Rabi’u Suleiman Bichi yace hukuncin kotun bai shafi dan takarar gwamnan ba, rikice ne na cikin gida daya haɗa ‘yan tsohuwar PDP da kuma ‘yan Kwankwasiyya.

Labarin da jaridar Daily Trust ta wallafa tace kotunta cire sunan Abba Kabir Yusuf tare da musanyashi da Dr Ibrahim Little.

Sai dai kuma a jiya ne Little da sauran ‘yan tsohuwar PDP suka sauya sheka daga PDP zuwa jami’iyyar APC.

“Jam’iyyar PDP reshen jihar Kano tana janyo hankalin al’umma cewa hukuncin da wata babbar kotu ta yanke a safiyar yau ya shafi jam’iyya ne kawai ba wai ɗan takarar gwamna ba. Kuma tuni jam’iyya ta daukaka ƙara akan wannan hukunci da aka yanke shi kuma ɗan takara zaici gaba da shirye-shiryensa na tunkarar zaɓe Mai zuwa na ranar asabar 9/03/2019.” – Rabi’u Bichi

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog