//

Masarautar Bichi tayi fatali da umarnin kotu, ta cire rawanin Sarkin Bai da wasu Hakimai 4

0

Majalisa masarautar bichi ta cire hakiman da basuyi mubayi’a ba ga Sarkin Bichi Alhaji Aminu Ado Bayero, a zaman ta na yau data gudanar a fadar masarautar Bichi.

Masarautar ta sanar da tsige dukkanin hakiman da basu yi wa masarautar mubaya’a ba.

Hakiman sun hada da Hakimin Bichi, Dambatta, Dawakin Tofa, Minjibir da Tsanyawa.

Bayan haka Majalisa ta ayyana maye guraben wadanda ta cire da mutane kamar haka;

  1. Abdulhamid Ado Bayero – Hakimin Bichi
  2. Mu’awiya Abbas Sunusi – Hakimin Tsanyawa
  3. Dr Abdullahi Mai Kano Rabiu – Dawakin Tofa
  4. Alhaji Wada Ibrahim – Dambatta
  5. Alhaji Isma’il Sarkin Fulani – Minjibir

Da Alhaji Labaran Abdullahi – Hakimin makoda.

Masarautar ta bayyana cewa sabbin nadin da ta kammala yi ya fara aiki “Nan take.”

Karin Labarai

Share.

Comments are closed.

%d bloggers like this:
©Dabo FM 2020